Monday, October 15, 2018

SIRRIN SHI'A

DAGA MURYAR ASH-SHEIKH ALBANIY ZARIA A CIKIN LAKCAN SHI MAI TAKEN MUNAFUNCI DODO NE VIA
SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA
..
ASH-SHEIKH ALBANIY ZARIA YACE; WAI SHIN ME YA KAWO WANNAN ZANGA-ZANGAR DA 'YAN SHI'A SUKE YI A DUK RANAR GOMA GA WATAN ALMUHARRAM????

...
Ash-Sheikh ya ci gaba da cewa; "Wai a yadda suka ce wai suna yin tane saboda tunanin bakin cikin kashe sayyidina Husaini 'dan gidan fatima da Aliyu a wannan ranar. Toh abun da muke cewa shine; Sayyidina Husaini ai be kai ubanshi Aliyu daraja ba.  Kamar yadda aka kashe Sayyidina Hussaini shima mahaifinshi Sayyidina Aliyu kashe shi aka yi. Kenan, idan dai soyayya ce tasa 'yan shi'a suke yi wa sayyidina Hussaini wannan zanga-zangar toh me yasa basa yima mahaifinshi Aliyu (RT) haka ba?
..
Amma 'yan shi'a suna da wani theory ne jama'a. Duk abun da suka san idan sun 'dauka bazai jawo musu abun da suke so ba toh baza su 'dauke shi ba. Inba haka ba Jama'a, Yadda aka yanka sayyidina Husaini, haka shima Sayyidina Aliyu Filla kanshi aka yi kan ya fadi gefe guda. Me yasa basa jimamin kisan sayyidina Ali?

..
Sannan sayyidina Hussaini ya kai darajar Annabi zakariyya da Annabi yahaya ne? Suma (su Annabi Zakariyya da Yahya) yanka su aka yi aka filla kansu. Shin me ya hana 'yan shi'a su rinka cika titi suna zanga zanga suna nuna jimamin ranar da aka kashe su?

..
Sheikh Albaniy ya cigaba da cewa; Jama'a ranar goma ga watan Almuharram ba ranar bakin ciki bace ko ka'dan. Haka kuma, ba ranar farin ciki bace ko ka'dan. Ranar ibada ce ta azumi *iyakanta kenan*. Abun da yazo kenan a cikin Hadisin Musnad na Imamu Ahmad, da Saheehu Bukhari, da Saheehu Muslim, da Sunani Abu Dawuda, da Muwadda na Imamu malik, da Sunanu Tirmizi da makamantan su. Abun da ya tabbata kenan (Ibadar Azumi ba wai zanga-zanga ba). Karanta littafin Sharhus-Sunnah ta Al-Imamu Muhyis-Sunnah Al-Hafizul Bagawiy. Don haka ba rana ce daza'a jaddada bakin ciki ba. Bashi daga cikin Sunnah jama'a bikin bakin ciki. Bashi daga cikin sunnah ace wai saboda wa'ni ya mutu rana kaza duk ranar in ta kewayo ace a taru wai yadda yasha wahala wurin ciwon 'dan kanoma a ranar kowa sai yasha tsamiya yasha tsamiya cikin shi ya za'ge shima yayi gudawa saboda sayyidina wa'ni ya mutu da gudawa a ranar, wannan ba sunnah bace. Haka bashi daga cikin Sunnah don an yanka Sayyidina Husaini a ranar Ashura kace wai a ranar Ashura sai kowa ya ji jiki.
..
Malam Albaniy ya cigaba da cewa; Wallahi a yau  zan gaya muku wata manufa a cikin fassarar munafunci dodo ne" Mecece manufar? Abunda 'yan shi'a suka ce shine; tunda wai har jinin Hussaini ya zuba a wannan ranar ta Ashura toh ayi duk yadda za ayi wata murmurda da sai an zubar da jinin makiya Sayyidina Huseini. Su waye suke cema makiya Hussaini? Wai mu Ahlussunnah mu ne makiya Sayyidina Husaini.

A gidan uwar wa aka ce muku bama tare da Huseini? Mune muke tare da Huseini domin mune muka ruwaito hadisin da Abdullahi 'dan Umar yana zaune sai wani yazo ya tambaye shi yace Alagafarta malam na 'dauki haramar aikin hajji sai sauro yazo ya tsaya min a jikin harami na sai na bige shi sai jin sauron ya 'bata min farin yadin harami na, ina hukuncin wannan jinin? Sai Abdullahi 'dan Umar yace ma mai tambayar shin kai ba mutumin 'kasar Iraqi bane? Sai mai tambayar Yace eh ni mutumin Iraqi ne. Sai Abdullahi 'dan Umar yace tashi ka bani wuri, kun zubar da jin jikan manzon Allah bai dame ka ba sai jinin sauro? Hadisin Saheehun Akhrajahul Imamul Tirmizi Fil Jami'i. Mu zaku gayama darajar Sayyidina Huseini? Sai Sayyidina Abdullahi 'dan Umar yace manzon Allah (SAW) wata rana ana cikin huduba ta jumma'a sai ga Hassan da Huseini sun taho uwar su Fatima ta shirya su ma'ana ta yi musu kwalliyar jumma. Sai ya gansu sun taho suna sheqi, yace sai ya kasa mallakar kan shi, sai ya yanke hudubar ya sauka daga kan mimbarin yaje ya tarbo su yazo ya  zauna dafa'an akan mimbara  ya 'dora wannan a dama wannan a hagu. Sai yace humaa raihanatan, yace wadannan su ne turare ne, wadannan su ne 'kanshi na, wadannan sune kwanciyar hankali na, wanda ke so na ya so su, wanda ke 'kin su toh ya 'ki ni. Mu Ahlussunnah mu muka ruwaito wannan hadisin. Zaku nuna mana darajar Sayyidina Huseini? Baza ku nuna mana darajar sayyidina Huseini ba.
..
ALLAHU AKBAR! ALLAH TA'ALA MUKE ROKO DA YA AMSHI SHAHADAR MALLAM.

No comments:

Post a Comment

The Big Bang Theory - Islamic perspective.

One of the great mysteries facing scientists today are the answers to the two following questions:   1. WHAT IS THE ORIGIN OF THE UNIV...